📚🖍Darul Fikr Na Mahdi Sanda 📚🖍
رفتن به کانال در Telegram
وَأَعِدُّوا لَهُم مَّا اسْتَطَعْتُم مِّن قُوَّةٍ.......! #Fikira_Ruhi_Jiki. #Kai_Da_Jama'a.
نمایش بیشتر824
مشترکین
-124 ساعت
-17 روز
+730 روز
در حال بارگذاری دادهها
کانالهای مشابه
هیچ دادهای
مشکلی وجود دارد؟ لطفاً صفحه را تازه کنید یا با مدیر پشتیبانی ما تماس بگیرید.
ابر برچسبها
هیچ دادهای
مشکلی وجود دارد؟ لطفاً صفحه را تازه کنید یا با مدیر پشتیبانی ما تماس بگیرید.
اشارات ورودی و خروجی
---
---
---
---
---
---
جذب مشترکین
نوامبر '26نوامبر '26
نوامبر '26
+2
در 0 کانالها
اکتبر '26
+18
در 0 کانالها
Get PRO
سپتامبر '26
+25
در 0 کانالها
Get PRO
اوت '26
+10
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئیه '26
+4
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئن '26
+6
در 0 کانالها
Get PRO
مه '26
+4
در 0 کانالها
Get PRO
آوریل '26
+4
در 0 کانالها
Get PRO
مارس '26
+23
در 0 کانالها
Get PRO
فوریه '26
+4
در 0 کانالها
Get PRO
ژانویه '26
+12
در 0 کانالها
Get PRO
دسامبر '25
+33
در 1 کانالها
Get PRO
نوامبر '25
+20
در 0 کانالها
Get PRO
اکتبر '25
+113
در 0 کانالها
Get PRO
سپتامبر '25
+9
در 0 کانالها
Get PRO
اوت '25
+7
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئیه '25
+7
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئن '25
+20
در 0 کانالها
Get PRO
مه '25
+15
در 0 کانالها
Get PRO
آوریل '25
+18
در 0 کانالها
Get PRO
مارس '25
+5
در 0 کانالها
Get PRO
فوریه '25
+18
در 0 کانالها
Get PRO
ژانویه '25
+5
در 0 کانالها
Get PRO
دسامبر '24
+15
در 0 کانالها
Get PRO
نوامبر '24
+23
در 0 کانالها
Get PRO
اکتبر '24
+17
در 0 کانالها
Get PRO
سپتامبر '24
+125
در 0 کانالها
Get PRO
اوت '24
+120
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئیه '24
+21
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئن '24
+17
در 0 کانالها
Get PRO
مه '24
+26
در 0 کانالها
Get PRO
آوریل '24
+27
در 0 کانالها
Get PRO
مارس '24
+9
در 0 کانالها
Get PRO
فوریه '24
+7
در 0 کانالها
Get PRO
ژانویه '24
+26
در 0 کانالها
Get PRO
دسامبر '23
+8
در 0 کانالها
Get PRO
نوامبر '23
+4
در 0 کانالها
Get PRO
اکتبر '23
+5
در 0 کانالها
Get PRO
سپتامبر '230
در 0 کانالها
Get PRO
اوت '23
+4
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئیه '23
+3
در 0 کانالها
Get PRO
ژوئن '23
+5
در 0 کانالها
Get PRO
مه '23
+4
در 0 کانالها
Get PRO
آوریل '23
+1
در 0 کانالها
Get PRO
مارس '23
+10
در 0 کانالها
Get PRO
فوریه '23
+7
در 0 کانالها
Get PRO
ژانویه '23
+25
در 0 کانالها
Get PRO
دسامبر '22
+17
در 0 کانالها
Get PRO
نوامبر '22
+274
در 0 کانالها
| تاریخ | رشد مشترکین | اشارات | کانالها | |
| 06 نوامبر | 0 | |||
| 05 نوامبر | 0 | |||
| 04 نوامبر | +1 | |||
| 03 نوامبر | 0 | |||
| 02 نوامبر | +1 | |||
| 01 نوامبر | 0 |
پستهای کانال
JIGON RAYUWA: KA YANKE MATSAYA MAI KYAU, KA TSAYA KANTA.
Na ci karo da wani baiti sai naga dacewar nazarinsa don amfaninmu a rayuwa.
إِذا كُنتَ ذا رَأيٍ فَكُنْ ذا عَزيمَةٍ
فَإِنَّ فَسادَ الرَّأيِ أَنْ تَتَرَدَّدا
Idan kana da ra'ayi, ka kasance mai azama, domin ɓarnar ra'ayi ita ce jinkiri a kokwanto.
Abin da ya kamata mu lura shine, Rayuwa ba ta jira mai jinkiri.
Mutane da yawa suna da ra'ayi mai kyau, suna da burin gyara, suna da niyyar zama nagari. Amma saboda jinkiri, sai burin ya mutu kafin a haife shi. Sai su zama mutanen da suke cewa "da na sani, da na yi", amma lokaci ya wuce.
Azama ita ce abin da ke raba shugaba da mabiyi. Shugaba ba shi ne wanda ya fi kowa ilimi ba, shi ne wanda da zarar ya ga gaskiya, sai ya tsaya a kai duk da tsoro, duk da maganar mutane, duk da tsada.
Ba zaka rubuta tarihi da abin da ka yi niyyar yi ba. Zaka rubuta shi da abin da ka yi azama ka kammala. Jinkirinka yau, zai zama nadamar ka gobe, abin na iya shafar ƴar ƴar da jikokinka gobe.
Don haka, daga yau, ka ɗauki wannan ka'ida:
1_ Ka yi tunani kafin ka yanke hukunci.
2_ Ka yi shawara da ƴan uwanka.
3_ Da zarar ka yanke, ka zama dutse. Kada ka jinkirta.
Kada ka bar tsoro ya rubuta tarihin ka. Ka rubuta shi da azama. Idan kana da ra'ayi? To ka kasance mai azama.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda
| 2 | "Shekarunka Tarihi ne da za'a karanta shi a bayan baka, sai kayi duba dame kake rubuta Tarihin."
_Mahdi Dahiru Sanda
4/11/2026
https://t.me/Mahdisanda | 13 |
| 3 | A addinin Allah ba a jarabci wasu kamar Ahlul-Baiti (A.S) da Shi'arsu ba. Wannan na kara mana tabbacin imaninsu, dama Allah (T) Ya ce ba a yin imani face sai ya biyo da jarabawa a bayansa, ko a rai, ko a dukiya, da sauransu.
_Mahdi Dahiru Sanda | 28 |
| 4 | Shin kai Musulmi ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku Musulmai ne? Ko kai Kirista ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku Kiristoci ne?
Shin kai dan Sunnah ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku 'yan Sunnah ne?
Shin kai dan Shi'a ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku 'yan Shi'a ne?
Shin kai abin da kake ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku sun yi ne?
Ko kuwa a'a, ka nemi sani, ka yi bincike, ka yi tunani, a kan abin da ka binciko ne ka rike abin da kake kai bisa dalili? Idan haka ne, masha Allah, ka yi abin da Allah Ya umurci masu hankali, kana da cikakken Uzuri.
Idan kuma ba haka ba ne, tir da kai, kana a sahun wadanda Allah Ya zarga. Yi sauri ka fita zuwa neman gaskiya, don neman Uzuri gaban Allah (T).
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا مَا أَنزَلَ اللَّـهُ قَالُوا بَلْ نَتَّبِعُ مَا أَلْفَيْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا ۗ أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ شَيْئًا وَلَا يَهْتَدُونَ.
"Kuma idan aka ce musu: 'Ku bi abin da Allah Ya saukar', sai su ce: 'A'a, za mu bi abin da muka samu iyayenmu a kai.' Ashe ko da Shaidan na kiransu zuwa ga azabar wuta mai ruruwa?" Suratul Luqman, Aya ta 21.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 41 |
| 5 | بدون متن... | 36 |
| 6 | Shin kai Musulmi ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku Musulmai ne? Ko kai Kirista ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku Kiristoci ne?
Shin kai dan Sunnah ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku 'yan Sunnah ne?
Shin kai dan Shi'a ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku 'yan Shi'a ne?
Shin kai abin da kake ne don babanka da kakanka da iyalinka da 'yan garinku sun yi ne?
Ko kuwa a'a, ka nemi sani, ka yi bincike, ka yi tunani, a kan abin da ka binciko ne ka rike abin da kake kai bisa dalili? Idan haka ne, masha Allah, ka yi abin da Allah Ya umurci masu hankali, kana da cikakken Uzuri.
Idan kuma ba haka ba ne, tir da kai, kana a sahun wadanda Allah Ya zarga. Yi sauri ka fita zuwa neman gaskiya, don neman Uzuri gaban Allah (T).
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا مَا أَنزَلَ اللَّـهُ قَالُوا بَلْ نَتَّبِعُ مَا أَلْفَيْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا ۗ أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ شَيْئًا وَلَا يَهْتَدُونَ.
"Kuma idan aka ce musu: 'Ku bi abin da Allah Ya saukar', sai su ce: 'A'a, za mu bi abin da muka samu iyayenmu a kai.' Ashe ko da Shaidan na kiransu zuwa ga azabar wuta mai ruruwa?" Suratul Luqman, Aya ta 21.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 1 |
| 7 | Zuciyata na cewa, in ba ka son wulakanci da tozarci, to ka tsarkake ni daga kaunar alatun duniya, musamman kudi da mata (ta hanyar da ba ta Shari'a ba).
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 36 |
| 8 | Rayuwa na cike da ƙalubale, Ina Girma ina ƙara fahimtar cewa ta'allaƙur Zuciya da wani abu ba Allah ba, da abinda ke da alaƙa da shi, to wannan ta'allaƙuwar fitina ce babba, tsira sai wanda Allah ya tsamar.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 36 |
| 9 | Mun koya daga jagororin Hamas (Allah Ya jikan magabata Ya karfafa na raye) cewa idan za ka yi aiki ka yi don Allah (T), kada ka fasa saboda al'ummar da kake kokarin karewa da samarwa 'yanci da karama ta kaskanta ka ta wofintar da kai.
_Mahdi Dahiru Sanda | 44 |
| 10 | A yayin sauke wazifa a tafarkin Allah, ana yi ne dai-dai da yadda zarafi suka ba da har zuwa ga nasara. Abin na bukatar basira da hakuri da juriya. Idan ka zabi Allah, dole ka yafe abin da ba Shi ba.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 38 |
| 11 | هذا هو الرجل الذي اتهموه بالجنون .. وقالوا لا يعبأ بشعبه .. الآن بعد ٥ سنوات نرى وجهاً آخر لم يره أحدنا يوماً .. الرجل يبكي دمعاً بوقف اطلاق النـ.. ـار عام ٢٠٢١ .. هؤلاء رجالٌ يريدون أن يصنعوا الحياة .. لكن يصنعوها كريمةً .. لا يرضوا عيش الذل ولا طعم الهوان ..
هذا الذي يعجز عن فهمه من باعوا كرامتهم بثمن بخسً .. وقبلوا بفتات الحياة .. ثم اطلقوا ألسنتهم في عرض أشرف أهل الأرض
لا تَسقِني ماءَ الحَياةِ بِذِلَّةٍ
بَل فَاِسقِني بِالعِزِّ كَأسَ الحَنظَلِ
رحم الله صاحب الفؤاد الحَي | 31 |
| 12 | A yayin sauke wazifa a tafarkin Allah, ana yi ne dai-dai da yadda zarafi suka ba da har zuwa ga nasara. Abin na bukatar basira da hakuri da juriya. Idan ka zabi Allah, dole ka yafe abin da ba Shi ba.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 1 |
| 13 | SUNATA KAFIRTA MASUSSUKA AMMA...!!!
Shi Mal. Masussuka da ire-irensa cewa sukayi, wannan Hadisan da ake jingina wa Annabi (S) basu yadda da su ba, a lura da kyau, ba su karyata Annabi (S) kai tsaye ba (To haka kun bashi hukumcin kafiri zindiqi).
Shi kuma Khalifa Thaani, sai da Annabi (S) ya kalle su ido da ido yayi Umurni ya ce ku kawo in rubuta muku abin da idan kuka rike ba za ku bata ba a bayana, ya kalli idon Annabi (S) ya ce masa "MU LITTAFIN ALLAH YA ISHE MU", to da shi da su Masussuka wa ya fi cancantar kalmomin da kuke jifar su Masussuka da su?
Mulahaza:
A lura, duka biyun ba ma tare da ra'ayinsu, mu bama raba bukatarmu ga Littafin Allah da bukatarmu ga Zantukan Hujjar Allah Annabi (S) ko Imami (A.s). Amma kashe Masussuka ba karabtarwar Musulumci bace, karabtarwar Musulumci itace tattaunawa da gabatar da hujjoji, kum kashe shi zalunci ne.
_Mahdi Dahiru Sanda
30/10/2026
https://t.me/Mahdisanda | 36 |
| 14 | Daya daga cikin Malamaina da nayi karatun Fiqihu da Tarbiyatul Islamiyyah a gurinsu, tare da amfanuwa da muhadarorinsa a munasabobi, da ta'alimomi da kuma Tafsirin Qur'ani da yayi gabatarwa a watan Ramadan na shekara-shekara. Mun koyi darasin Akhlaq daga gunsa a aikace ta yadda in muka ji kissoshin A'Imma (A.s) akan Akhlaq dinsu yakan Halarto a kwakwalwarmu, domin koyinsa da dabi'un.
Jarumtarsa da sadaukarwarsa, da Ikhlasin sa, da sallamawa Allah, wasu abubuwa ne da basu buya a rayuwarsa mai albarka.
Har wayau shi ubane a garemu, Shaheed Sheikh Qasim Bn Umar (R), yau 19 Jimada Ula yake cika shekara 8 da Shahada, mu karanta fatiha da salati hadiya zuwa ga Ruhinsa mai tsarki.
_Mahdi Dahiru Sanda
30/10/2026 | 36 |
| 15 | Ba muna tare da Marigayi Mal. Masussuka bane a tafiyarsa ta Al-Qur'ani zalla ba, a'a mu mun yarda da Al-Qur'ani da samuwar ingantattun zantukan Annabi (S), muna riko da su da kasancewar su daga Annabi (S), muna kuma watsi da marasa nagarta a sakon su ko da Isnadinsu ya inganta.
Amma muna tare da shi ne a kokarinsa na samar da yanayi da zai baiwa kowa 'yancin yin fahimtarsa kuma a aikace don zaman lafiya, da kuma dusashe kaifin kafirta mutane da halasta jinin su da Wahabiyawa, Salafawa, lakurawan birni da na kauye ke yi, wanda aiki ne na America da Isra'ila a cikin Musulmi suke aiwatarwa. Don haka manufarsa ta wannan janibin daidatacciya ce.
Aqidarsa kuwa a iya abin da muka riska shi ne ba daidai ba ne, kuma da mun riske zaman ta daidai da mun rike ta hannu biyu, dan idan ba mu yi ba to ba mu da uzuri a gaban Allah. Amma shi a yayin da Allah ya kalli zuciyarsa da hankalinsa ya zama lallai iya abin da ya iya riska kenan gwargwadon ikonsa, to lallai mai uzuri ne a gaban Allah.
Irin wannan mauqifin muna da shi har a matakin Muqawama a fadin duniya. 'Yan Huthi a Yamen, a Aqidarsu ta Shi'a Zaidiyya a matsayinmu na Imamiyya muna kallon rashin ingancinta da zaman ta ba shiriya ba, su ma za su iya samun uzuri in ya zama su iya abin da suka iya riska kenan. Amma mu da muka fi gamsuwa da dalilan Imamiyya ba mu da uzurin riko da wani abu koma bayan wannan, amma mauqifin 'Yan Huthi a siyasa da Muqawama daidaitacce ne kuma shiriya ne, sai ya zama ta wannan jihar muna tare da su dari bisa dari.
Wannan shi ne Ta'assubanci mai kyau, wato kasancewa da dai-dai da gaskiya a inda duk ta bayyana.
Allah ya karya Amurka da Israel da karnukansu na ciki da waje, masu aiki bisa sani ko bisa jahilci.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 44 |
| 16 | بدون متن... | 35 |
| 17 | Ba muna tare da Marigayi Mal. Masussuka bane a tafiyarsa ta Al-Qur'ani zalla ba, a'a mu mun yarda da Al-Qur'ani da samuwar ingantattun zantukan Annabi (S), muna riko da su da kasancewar su daga Annabi (S), muna kuma watsi da marasa nagarta a sakon su ko da Isnadinsu ya inganta.
Amma muna tare da shi ne a kokarinsa na samar da yanayi da zai baiwa kowa 'yancin yin fahimtarsa kuma a aikace don zaman lafiya, da kuma dusashe kaifin kafirta mutane da halasta jinin su da Wahabiyawa, Salafawa, lakurawan birni da na kauye ke yi, wanda aiki ne na America da Isra'ila a cikin Musulmi suke aiwatarwa. Don haka manufarsa ta wannan janibin daidatacciya ce.
Aqidarsa kuwa a iya abin da muka riska shi ne ba daidai ba ne, kuma da mun riske zaman ta daidai da mun rike ta hannu biyu, dan idan ba mu yi ba to ba mu da uzuri a gaban Allah. Amma shi a yayin da Allah ya kalli zuciyarsa da hankalinsa ya zama lallai iya abin da ya iya riska kenan gwargwadon ikonsa, to lallai mai uzuri ne a gaban Allah.
Irin wannan mauqifin muna da shi har a matakin Muqawama a fadin duniya. 'Yan Huthi a Yamen, a Aqidarsu ta Shi'a Zaidiyya a matsayinmu na Imamiyya muna kallon rashin ingancinta da zaman ta ba shiriya ba, su ma za su iya samun uzuri in ya zama su iya abin da suka iya riska kenan. Amma mu da muka fi gamsuwa da dalilan Imamiyya ba mu da uzurin riko da wani abu koma bayan wannan, amma mauqifin 'Yan Huthi a siyasa da Muqawama daidaitacce ne kuma shiriya ne, sai ya zama ta wannan jihar muna tare da su dari bisa dari.
Wannan shi ne Ta'assubanci mai kyau, wato kasancewa da dai-dai da gaskiya a inda duk ta bayyana.
Allah ya karya Amurka da Israel da karnukansu na ciki da waje, masu aiki bisa sani ko bisa jahilci.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda | 2 |
| 18 | MUSULUMCI BA SUNAN DA ZA'A YI AMFANI DA SHI WAJEN HALATTA ZALUNCI DA TA'ADDANCI BA NE!!!.
Annabi Muhammad (S) bai taɓa kashe wani saboda kawai aqidarsa ko addininsa ba. Yaƙin da ya yi da waɗanda suka yaƙe shi, ya yi ne a matsayin wanda ake kai wa hari, domin kare kansa da al'ummarsa. Amma mushirikai waɗanda ba su taɓa cutar da Annabi (S) ba, ba su ɗauki takobi domin yaƙar Musulunci da Musulmai ba, kuma suka nemi zaman lafiya, Annabi (S) ya ba su damar rayuwa bisa fahimtarsu da aqidarsu, ba tare da tilasta musu shiga Musulunci ba. Kai, har ma ya hana Musulmai zagin abubuwan bautar da suke bautawa!, idan wani Musulmi ya kuskure ya kashe wani a cikin mushrikan masu zaman lafiya da musulmai, Annabi (S) ma yakan biya diyarsa ne da kansa.
Don haka, kada ka jingina wa Annabi (S) wata Sunnah ta kashe wanda ya saɓa maka a aqidarka kawai saboda saɓanin aqida. Ka yi Umawiyancinka, ka yi Sahyuniyancinka, ka yi Amerikancinka, amma kada ka lulluɓe waɗannan ayyukan naka da rigar Annabi Muhammad (S), kana mai kiran ayyukan naka da Musulunci!
Musulunci ba sunan da za a yi amfani da shi wajen halatta zalunci da ta'addanci ba ne.
_Mahdi Dahiru Sanda
27/10/2026
https://t.me/Mahdisanda | 50 |
| 19 | بدون متن... | 45 |
| 20 | Addinin bai koyar da kashe wani sabida Aqidarsa ba, ya koyar da fuskantar fahimta ne da dalili da hujjah, kashe wani sabida Aqidarsa Ta'addanci ne, Zalumci ne wanda aka kashe Mazlumi ne.
_Mahdi Dahiru Sanda
27/10/2026
https://t.me/Mahdisanda | 65 |
