Ana hasashe cewa nan da shekaru hudu 4 masu zuwa (2030) kudaden da za'a zuba a cikin tokenized RWA wato (Real World Assets) zasu zarce Dala trillion goma, wato Naira quadrillion 13,150,000,000,000,000 a kudin Nigeria a yau.
A yanzu kudaden da suke cikin tokenized RWA sun kai Dala biliyan dari 320. Wato Naira trillion dari 434. Gwamnatin Amurka tana kan gaba wajen tokenizing Government Bonds da kuma digital treasury yanzu haka.
Blockchain na Ethereum shi yake da 48 percent na dukkan kudaden da aka zuba a RWA a fadin duniya, sai wasu BNB (Binance blockchain) da kuma Solana.
A cikin fasahar tokenized assets ana iya saka gida a kasuwa ko a haya (Rent) ko kuma wani hotel, ko fine arts da sauran su. Misali;
Hotel din Sheraton, ko Tahir Guest Palace sai ayi tokenizing dinsu, a saka su a kasuwa, sai ayi minting dinsu akan blockchain, sai a samar da token na RWA domin wadanda suke son saya. Abinda yake faruwa a nan shine;
Idan aka saka Tahir Guest Palace a kasuwa, misali. Aka ce ana neman mai son karban haya (Rent) za'a dauki lokaci mai tsawo kafin a samu mai biya, saboda girman asset din, kudi ne mai yawan gaske in billions. Toh waye zai iya daukan billions ya karbi haya?
To idan aka yi tokenizing Tahir Guest Palace misali, zaka iya zuwa ka sayi wani bangare na asset din, idan anyi masa kudi Naira biliyan 100 ne toh zaka iya zuwa ka sayi na Naira dubu 50,000 rak. Wani kuma zai sayi na Naira miliyan 10, wani Naira dubu dari 500k.
Toh a haka har za'a saye token din gaba daya, sai ya zama anyi raising Naira biliyan 100 din. Daga nan kuma management din zasu cigaba da gudanar dashi, duk abinda aka samu na riba za'a buga percentage dinka a dinga biyan ka kullum, ko duk sati, duk wata ko duk shekara. Gwargwadon yadda ka zaba.
Abubuwan lura a nan shine;
1. Tahir Guest Palace ya tashi daga kadarar da sai irin su Aliko Dangote ne kadai zasu iya zuba jarin su zuwa kadarar da mai dubu 50,000 da mai miliyan 100 zasu hadu a cikin sa, kuma kowa yana samun percentage dinsa.
2. Daga ko ina a duniya zaka iya, wanda yake London zai iya saya, wanda yake Saudi Arebia, wanda yake Bauchi ko Jigawa ko Maiduguri duk zasu iya saya.
3. Zaka iya siyar da percentage dinka a kowane lokaci, zaka saka shi a P2P marketplace nan take a saya a baka kudin ka.
4. Za'a dinga biyan ka da kudin kasar ka ko USDT ko USDC ko Bitcoin ko Ethereum ko Solana.
5. Sannan darajar asset din dake physical wato zahiri dai dai yake da wanda yake online.
Wannan kadan ne daga cikin yadda ake gudanar da tokenized Real World Assets ko RWA a yau.
Hatta stock market yanzu da sauran commodities zaka ga ana tokenizing dinsu kuma wata duniya ce mai girma da fadin gaske.
Tambayar a nan, shin ya halaccin irin wannan a Musulunci? akwai dalilan da zasu iya halatta ko haramta irin wannan?
Zamu amsa wadannan tambayoyin, in sha Allah.