cookie

Ми використовуємо файли cookie для покращення вашого досвіду перегляду. Натиснувши «Прийняти все», ви погоджуєтеся на використання файлів cookie.

avatar

Zauren Abba Lawan Hassan {Abu Aysha} الكلمة الطيبة صدقة

Neman ilimi wajibi ne a kan dukkan Musulmi da Musulma

Більше
Рекламні дописи
265
Підписники
+124 години
+47 днів
+830 днів

Триває завантаження даних...

Приріст підписників

Триває завантаження даних...

*🌲HANYOYI ƊARI (100)🌲* *GA MAI NEMAN* *🌲RAYUWA TA GARI 🌲* *Hanya ta (38-C): Neman ilimi:* 👉🏼 Bisa ga haka neman ilimi da kuma yãɗa ilimi bai keɓanci wasu mutãne ne banda wasu ba, don cikin magabata na kwarai tun daga kan Sahabbai da Tãbi’ai; sun kasance suna neman ilimi kuma sunã yãɗa ilimin don Allah kawai ba don neman abin duniya ba. ✍🏼 Don haka ya wajaba a kan muminai su ɗauka cewa neman ilimi da aiki da shi dõle ne a kan su daidai gwargwadon iko, ba kuma ɗaukar shi ilimin addini da niyyar hanyar cin abinci ba, in an yi don Allah; to, zai sawwaƙewa bãwan hanyar arzƙi. 👉🏼 Sã’ilin nan shi ilimi fãɗi ne da shi, bisa ga haka duk ilimi wanda zai amfãni al’umma shi ake buƙãta da mu nema, duk da cewa shi kansa ilimi na neman duniya shi kansa wani sãshi yãfi amfãni a kan wani sãshin, kamar ilimin likitanci ga ƴã mace shi yafi mata amfãni da aikin banki, to, haka ma ga sauran ilimai. ✍🏼 Duk ilimin da bãyi za suyi, abin da ake so a nemi ilimin don Allah kawai ba don me za a sãmu ba; don duk wanda ya bi Allah da taƙawa, lalle Allah zai buɗe masa hanyõyin arziƙi ta inda bãwan bai ma sani ba. *Allah ya dãtar da mu* 👍🏼 Kasance da mu a Facebook 👇🏼 https://www.facebook.com/102613724899406?referrer=whatsapp 👍🏼Ko Telegram 👇🏼 https://t.me/AbbaLHassan 👍🏼 Ko WhatsApp Maza 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/LUfFNtKFd7P7SoMsV55IoB 👍🏼 Ko WhatsApp Mata 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/EludpAiBvfF1BmwhrzkDzS *📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}*
Показати все...
*🌲HANYOYI ƊARI (100)🌲* *GA MAI NEMAN* *🌲RAYUWA TA GARI 🌲* *Hanya ta (38-B): Neman ilimi:* 👉🏼 Wani mutum ya yiwa Umar ɗan Abdul’aziz (RH) wa’azi cikin wa’azin nasa yake cewa: “Idan har za ka iya zama Malami; to, ka zamanto Malami, idan kuma ba za ka iya zama Malami ba; to, ka kasance mai neman ilimi, idan ba za ka iya zama mai neman ilimi ba; to, ka so/ƙaunaci Malamai, idan ba za ka iya hakan ba; to, kada ka tsani/ƙyãmace su”. ✍🏼 Imãm Hasanul Basry (RH) yana cewa: “Mutum ya kan kasance mai neman ilimi kuma ba ya jimãwa cikin hakan fãce sai an ga wannan ilimi a tattare da shi ta wajen/ɓangaren jin tsoron Allah da harshensa da idonsa da hannunsa da sallarsa da maganarsa da gudun duniyarsa…” 👉🏼 Sã’ilin nan shi Mumini shi ne wanda ba ya daina neman ilimi har mutuwa, kuma yana mai girmama wanda yake koyon ilimin a wajensa, kuma yana girmama mãsu ilimi, don fa shi abu ne mai daraja kamar yadda Allah (SWT) yake cewa: 📚 ((…Ka ce, “Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba? Mãsu hankali kwai ke yin tunãni)). 📚 Da kuma faɗinsa (SWT): ((…Malamai kwai ke tsõron Allah daga cikin bãyinSa. Lalle, Allah, Mabuwãyi ne, Mai gãrafa)). *Allah ya dãtar da mu* 👍🏼 Kasance da mu a Facebook 👇🏼 https://www.facebook.com/102613724899406?referrer=whatsapp 👍🏼Ko Telegram 👇🏼 https://t.me/AbbaLHassan 👍🏼 Ko WhatsApp Maza 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/LUfFNtKFd7P7SoMsV55IoB 👍🏼 Ko WhatsApp Mata 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/EludpAiBvfF1BmwhrzkDzS *📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}*
Показати все...
*🌲HANYOYI ƊARI (100)🌲* *GA MAI NEMAN* *🌲RAYUWA TA GARI 🌲* *Hanya ta (38-A): Neman ilimi:* 📚 Ya zo a Hadisin da aka karɓo daga Abid Dardã’i (RA) yace: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: ((Duk wanda ya bi wata hanya yana mai neman ilimi a cikinta, Allah zai biyar/shiryar da shi hanyar shiga Aljanna. Kuma lalle Malã’iku na sanya/ajiye fukãfukansu ga mai neman ilimi, kuma lalle Malami duk abin da ke sammai da duk abin da ke ƙasa har kifãye da ke cikin ruwa sunã neman masa gãfara… 📚 Kuma girma/darajar/falalar Malami a kan mai bauta kamar falalar watã ne a kan sauran taurãri, lalle Malamai su ne magãda Annabawa, lalle su Annabawa ba su bar gãdon Dinãre ko Dirhami ba; kawai abin da suka bar gãdo shi ne ilimi, duk wanda ya riƙe shi to, yayi riƙo da rabo mai yalwa/girma/fãɗi)). Imãm Abu Dãwud da At Tirmizy. ✍🏼 Neman ilimi na cikin mafi girman ibãdu har ma yãfi nãfila a lõkacin da jãhilci ya yawaita kuma Malamai suka yi ƙaranci, kuma ƙirƙirarrun abubuwa suka yawaita, har ya zaman to mutãne suna bin wannan abubuwan. 👉🏼 Kuma neman ilimi wãjibi/dõle ne a kan dukkan Musulmai, namiji ko mace su san abin da zai wadãtar da su wajen sauke nauyin shari’a da ke kansu, da kuma sanin Ubangiji domin bauta masa cikin ilimi. *Allah ya dãtar da mu* 👍🏼 Kasance da mu a Facebook 👇🏼 https://www.facebook.com/102613724899406?referrer=whatsapp 👍🏼Ko Telegram 👇🏼 https://t.me/AbbaLHassan 👍🏼 Ko WhatsApp Maza 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/LUfFNtKFd7P7SoMsV55IoB 👍🏼 Ko WhatsApp Mata 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/EludpAiBvfF1BmwhrzkDzS *📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}*
Показати все...
Dandalin kyakkyawar kalma sadaka ce

Dandalin kyakkyawar kalma sadaka ce. 2,997 likes · 12 talking about this. Assalamu Alaikum An samar da wannan dandali ne don gabatar da abin da ya shafi addinin Musulunci don samun rayuwa mai kyau a...

*🌲HANYOYI ƊARI (100)🌲* *GA MAI NEMAN* *🌲RAYUWA TA GARI 🌲* *Hanya ta (37-B): Karãtun Alƙur’ãni mai girma:* 👉🏼 Bisa ga haka, ibãda wajen karãtun Alƙur’ãni kala-kala ne/ce: akwai tilãwa/karantãwa da Alƙur’ãni, sai kuma da ka/hadda, da kuma rera shi, da karãtun Alƙur’ãni cikin sallah, da kuma lõkuta daban-daban da kuma saurãran Alƙur’ãnin. ✍🏼 Sã’ilin nan kõyansa da kõyar da shi, da sanin tafsirinsa/ma’anarsa da ma sauran ilimin da yake da alãƙa da shi Alƙur’ãnin, duk waɗannan na cikin ibãda, haka ma kuma girmama littãfin Allah (SWT); to, girmama Allah ne, kuma a wurin Allah lãda mai yawa yake. 👉🏼 Sayyidna Umar ɗan Kaɗɗab (RA) ya kasance yana cewa da Abi Musa Al’ash’ary (RA): “Tunãtar da mu Ubangijinmu, sai ya yi karãtun Alƙur’ãni a wurin har sai lõkacin sallah ya kãwo/shiga. Sai a ce da Sayyidna Umar (RA) Yã Sarkin Muminai lõkacin sallah, lõkacin sallah, sai yace: shin yanzun ba a cikin sallar muke ba? Yana nuni ga faɗin Allah (SWT): 📚 ((…kuma lalle ambaton Allah ya fi girma…)). *Allah ya dãtar da mu* 👍🏼 Kasance da mu a Facebook 👇🏼 https://www.facebook.com/102613724899406?referrer=whatsapp 👍🏼Ko Telegram 👇🏼 https://t.me/AbbaLHassan 👍🏼 Ko WhatsApp Maza 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/LUfFNtKFd7P7SoMsV55IoB 👍🏼 Ko WhatsApp Mata 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/EludpAiBvfF1BmwhrzkDzS *📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}*
Показати все...
Dandalin kyakkyawar kalma sadaka ce

Dandalin kyakkyawar kalma sadaka ce. 2,997 likes · 12 talking about this. Assalamu Alaikum An samar da wannan dandali ne don gabatar da abin da ya shafi addinin Musulunci don samun rayuwa mai kyau a...

*🌲HANYOYI ƊARI (100)🌲* *GA MAI NEMAN* *🌲RAYUWA TA GARI 🌲* *Hanya ta (37-A): Karãtun Alƙur’ãni mai girma:* 📚 Ya zo a Hadisin da aka karɓo daga Abdurrahmãn ɗan Shibl (RA) daga Manzon Allah (SAW) yace: ((Ku karanta Alƙur’ãni kuma kuyi aiki da shi, kuma kada ku barshi/ƙin karantã shi, kuma kada ku wuce gõna da iri a cikinsa, kuma kada ku ci da shi, kuma kada ku karantã shi don sãmun wani abun duniya)). Imãm Ahmad, ɗabrãny, Baihaƙy da Abu Ya’ala. ✍🏼 Karãtun Alƙur’ãni na daga mafi girman ibãdu, kuma hanyã ce ta fuskantar umurnin Allah (SWT) wajen aikata abin da yayi umarni da shi. 👉🏼 Duk wanda ya wãtsar da karãtun Alƙur’ãni mai girma har zuwa wani lõkaci ba tãre da uziri ba; to, wannan ya jefar/wãtsar da shi kenan! ✍🏼 Sã’ilin nan karãtun Alƙur’ãni dõle ya zama anyi don Allah (SWT) ne, ba don alfahari ba da neman tãra dukiya ba da neman matsayi ba ko neman wani abu cikin duniya wanda sai ya ƙãre. 👉🏼 ƙetare iyãka ga Alƙur’ãni kuma shi ne riƙon ƙanƙamo bisa ga abin da bã haka shari’a ta kõyar ba, da kuma riƙon ƙanƙam cikin (Mutashãbih) da ke cikin sa. 📚 Allah (SWT) yana cewa: ((Ka ce: “Yã ku Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bã gaskiya ba, kuma kada ku bibiyi son zunciyõyin waɗansu mutãne waɗanda suka rigã suka ɓace a gabãni, kuma suka ɓatar da wasu mãsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya”)). *Allah ya dãtar da mu* 👍🏼 Kasance da mu a Facebook 👇🏼 https://www.facebook.com/102613724899406?referrer=whatsapp 👍🏼Ko Telegram 👇🏼 https://t.me/AbbaLHassan 👍🏼 Ko WhatsApp Maza 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/LUfFNtKFd7P7SoMsV55IoB 👍🏼 Ko WhatsApp Mata 👇🏼 https://chat.whatsapp.com/EludpAiBvfF1BmwhrzkDzS *📝Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}*
Показати все...
Dandalin kyakkyawar kalma sadaka ce

Dandalin kyakkyawar kalma sadaka ce. 2,997 likes · 12 talking about this. Assalamu Alaikum An samar da wannan dandali ne don gabatar da abin da ya shafi addinin Musulunci don samun rayuwa mai kyau a...

Оберіть інший тариф

На вашому тарифі доступна аналітика тільки для 5 каналів. Щоб отримати більше — оберіть інший тариф.